sun mutu sakamakon wani harin kwantan bauna da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai kan sojojin Najeriya a garin Domboa na jihar Borno, ranar Laraba.

Har wa yau, sojoji 12 sun yi batan dabo bayan harin na ranar Laraba, kamar yadda wata majiyar soji da ba ta son a ambaci sunanta ta shaida wa    Kaduna press ranar Alhamis.

"Mun rasa sojoji 10 a lokacin wani artabu da 'yan ta'adda da suka yi wa sojojinmu kwantan bauna yayin wani sintiri a yankin." In ji majiyar ta soja.

"An jikkata sojoji guda 9 sannan muna neman 12."

Sojojin Najeriya sun nesanta kansu daga bidiyon cin zarafi
Yadda Boko Haram ta yi wa sojoji kofar-rago a Borno
Sojojin dai sun fuskanci harin 'yan kungiyar ne lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa sansaninsu da ke Damboa mai nisan kilomita 88 daga birnin Maiduguri.

Yankin da aka kai harin na kusa da dajin Sambisa, wani wuri da ke karkashin ikon Abubakar Shekau.

Wata majiyar ta soji ta kara da cewa daukin badadin ya tilasta wa sojojin tserewa duk da cewa sun sami nasarar kisan 'yan kungiyar 9.

'Yan kungiyar sun kuma kone motocin sojoji sannan kuma sun yi awon gaba da mota kirar a kori-kura da kuma wasu bindigogi shida.

Kungiyar Boko Haram na kara yawaita hare-hare kan sojojin Najeriya tun watan Yunin 2018, inda kungiyar IS da ke yammacin Afirka ke daukar alhakin kai mafi yawancin hare-haren.