A yau Alhamis 14-11-2019 dai dai da 17 ga watan Rabi'ul Auwal, dubban yan'uwa Almajiran Sayyid Zakzaky sun fito dan jaddada bai'ar su, ga Annabi Muhammadu (s.a.w.a), kamar yadda a ka saba duk shekara yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky na fitowa dan murna da zagayowar da ranar da a ka haifi Manzon Allah (s.a.w.a).

To Alhamdu-lillah yau ma yan uwa na kaduna sun fito dan jaddada bai'ar su ga Manzon Tsira (S), yayi da a ka dago muzahara da ga Kano road da ke nan cikin garin Kaduna, a na tafe a na rera waken murnar da samuwar Manzon Allah (s.a.w.a). Da Karin kira ga wannan azzalumar gwamnatin da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da iyalansa.

Bayan an wuce shataletalen living tins an biyo ta mangal plaza an mike hanya, i sa yan timatir, kawai sai muka fara jin harbi ta ko i na, yan sandan metro ne, suka shawo gaban muzahara, ya yin da al'umma da ke gefen hanya suka fara jifan su, suna cewa: wannan zaluncin ya I sa haka, bama so, ku bar mu da abin da halin da kuka jefa mu.

Nan take suka bude wa jama'a wuta, suka tarwasta su. Sun harbi yan uwa hudu (4). Ba wanda yayi shahada sai dai a Kwai masu raunin da komai zai iya faruwa.


Muna rokon Allah ya ba su lafiya.

KNPRSCD 07 ✍️
Kaduna Press