Femi Falana ya shaida wa    Kaduna press  cewa Buhari na neman zango na uku ta hanyar sauya kundin tsarin mulki da zai ba shi damar tsawaita mulkin nasa.

A farkon watan Oktoban da ya gabata ne dai shugaba Buhari ya musanta rade-radin da wasu ke yi na batun sake neman wani wa'adin.

Mai magana da yawun shugaban, malam Garba Shehu ya ce "Shugaba Buhari na son kammala wa'adinsa na biyu da zai kare a 2023, lokacin da za a sake gudanar da wani babban zaben kuma ba zai sake tsayawa ba."

Amma Falana ya zayyana wasu abubuwa da ya ce dukkansu alamu ne na shugabanni masu tsawaita zamansu a kan karaga a kasashen yammacin Afirka, inda kuma ya ce suna faruwa a Najeriya.

Buhari ba ya sukar masu tsawaita mulki

Falana ya bayar da Misalai da wasu kasashe inda ya ce shugaba Patrice Talon na Benin ya mayar da kasar bisa tsarin mai jam'iyya daya, haka nan ma a Togo, ta yadda za su tsawaita mulkinsu, kuma Najeriya ba ta ce komai ba game da hakan.

Shugaba Alpha Conde na kasar Guinea shi ma ya kawar da duk wadanda yake ganin za su iya zama masa cikas domin tabbatar da aniyarsa ta yin mulki a wa'adi na uku, a Cote d'Ivoire ma abin da ke faruwa ke nan.

Femi Falana ya kara da cewa Najeriya ita ce jagorar kasashen yammacin nahiyar Afirka, amma ba ta nesanta kanta daga duk wadannan abubuwa da suka saba wa kundin tsarin mulki ba.

"Akwai dokokin kungiyar ECOWAS a kan demokuradiyya da shugabanci wadanda suka kyamaci duk wani yunkuri na sauya tsarin gwamnati ba bisa ka'ida ba."

"Bayan na yi la'akari da tarihin abubuwan da suka faru gare mu a baya da kuma abinda ke faruwa a yanzu, na yarda cewa lallai Buhari na son ya yi wa'adi na uku," in ji shi.

'Yancin kafafen yada labaru - Tsare Sowore

Falana ya ce a Najeriya, masu kare hakkin bil'adama sun ce alamu sun bayyana karara, domin duk gwamnatin da ta rufe bakin kafafen yada labaru, ta mayar da kasar mai bin tsarin jam'iyya daya, ta haramta zanga-zanga koda kuwa ta lumana ce, ta yi wa 'yan ta'adda afuwa, ta kuma rinka hantarar 'yan jarida, to gwamnati ce wadda ba ta martaba dokokin kasa.

"Hakan karan-tsaye ne ga kundin tsarin mulki kuma shiri ne na lalata al'amuran kasa da share hanyar yin tazarce a karo na uku."

Falana ya ce "Sun tsare Sowore ne domin su kashe jaridar Sahara reporters, domin Sahara reporters ta taka muhimmiyar rawa wajen dakile yunkurin Obasanjo na yin tazarce."

"Ina kare Sowore ne saboda babu wata hujja da ta tabbatar da zargin da suke masa na cin amanar kasa. Ina da hujjojina wadanda zan bayyana su nan ba da dadewa ba."

Wata jarida ta cikin gida ta yi zargin cewa a lokacin gwamnatin shugaba Buhari ne 'yan jarida suka fi shan wahala cikin shekara 34.

Sai dai shugaba Buhari a baya ya fito fili yana cewa gwamnatinsa tana martaba 'yancin yada labarai.

Rikici tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa

Falana ya dade yana sukar gwamnatocin Najeriya
Babban lauyan ya ce a duk lokacin da shugaban kasa ya tsangwami mataimakinsa, ya raunana karfinsa domin hana shi duk wani yunkuri na yin takara, hakan na nuna cewa akwai wani abu a karkashin kasa.

A makon da ya gabata ne aka rage 35 daga cikin masu taimaka wa mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo.

Sai dai Mallam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaba Buhari ya ce dalilin da ya sa aka rage ma'aikatan shi ne domin a rage yawan kudin da gwamnati ke kashewa, da kuma inganta hanyoyin tafiyar da al'amuran gwamnati.

Rashin biyayya ga hukuncin kotu

Femi Falana ya ce "Babu matakin da aka dauka kan masu yekuwar tazarce amma an kama wadanda ke neman a daina karya umurnin kotu."

"Babu wata gwamnati da za ta fito fili ta ce tana neman wa'adi na uku, mutane su ne za su gano da kansu ta hanyar la'akari da abubuwan da ke faruwa wadanda suka saba wa tsari na demokradiyya."

Ya ce tsarin mulkin 
Najeriya bai tanadi yin wa'adi na uku ga wanda ke kan kujerar shugabancin kasar ba.

KNPRSCD 08
Kaduna press