Masu zanga-zanga sun hau kan titunan kasar Iran domin nuna adawa da karin kudin mai
Ministan cikin gida na Iran ya yi gargadin cewa jami'an tsaro za su kara kaimi wajen dakile zanga-zangar da al'umma ke yi a kasar kan karin kudin man fetur.

Zanga-zangar ta balle ne a fadin kasar bayan da gwamnati ta sanar da karin kudin man fetur ba zato ba tsammani.

Mutum daya ne ya mutu yayin da wasu da dama suka samu rauni tun bayan ballewar zanga-zangar.

TALLA

Gwamnati ta ce wannan sauyi da aka samu a kudin man zai taimaka wajen samar da kudaden da za a tallafa wa talakawa.

Iran dai ta shiga halin tsaka-mai-wuya ne tun bayan da Amurka ta kakaba mata takunkumai na tattalin arziki bayan da shugaba Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran na shekarar 2015.

Tun a ranar juma'a ne zanga-zangar ta fara, awanni kadan bayan sanarwar sabbin tsare-tsare na gwamnatin kasar - Inda zanga-zangar ta ci gaba da yaduwa zuwa wasu biranen kasar a ranar Asabar.

Wasu rahotanni na cewa gwamnati ta sa linzami ga intanet na kasar, inda kafar dillancin labaru ta Reuters ta ce ta ga tawagar masu sanya ido kan yanar gizo.

Masu zanga-zanga na gangami har a Tehran, babban birnin kasar
Ministan cikin gida Abdolreza Rahmani-Fazli, a wata tattaunawa da kafar yada labarun kasar a ranar Asabar ya yi gargadin cewa babu makawa jami'an tsaro za su tashi tsaye domin dawo da lumana a fadin kasar.

Mista Rahmani-Fazli ya soki wasu da ya kira 'mutane 'yan kalilan' da ya ce sun kawo hargitsi cikin al'umma domin haifar da husuma.

Mene sabbin matakan?

A karkashin sabon tsarin, an kayyade cewa kowane mai mota zai iya shan lita 60 ne kacal na fetur a wata daya, kan kudi riyal 15,000 a kan kowace lita. Amma idan ya zarce yawan litar da aka kayyade, to za a ringa sayar masa ne a kan kudi riyal 30,000 a kan kowace lita.

A baya akan bar mai mota ya sha mai har lita 250 a wata guda, kan kudi riyal 10,000 a kan kowace lita, in ji kamfanin dillacin labaru na

Gwamnati ta ce za a yi amfani da kudin da aka tattara daga tallafin da aka cire ne wajen bayar da tallafin kudi ga marasa karfi.
Masu zanga-zanga a birnin Shiraz
Shugaban hukumar tsare-tsare da kasafin kudi na Iran Mohammad Baqer Nobakht ya ce daga wannan wata mutane miliyan 18 ne za su samu karin tallafin kudi a sanadiyyar wannan karin kudi na mai.

A wata hira da shi ta kafar talabijin na kasar, Nobakht ya ce ana sa ran tsarin zai samar wa kasar karin kudaden shiga har riyal tiriliyan 300 a kowace shekara.

Labaru daga
Kaduna press