Da yake bayani a gaban dubban mutane da suka taru a tsakiyar birnin Yazda yau Lahadi shugaban na kasar iran Hassan Rauhani ya bayyana cewa Iran ta gano wannan rijiyar mai din ne duk da matsin lamabar Amurka da mafiyawanci ya shafi bangaren man fetur dinta ne.

Ya kuma ci gaba da cewa filin da aka gano na man fetur din ya kai fadin mita murabba’in mita 2400, kana kuma zurfinsa ya kai mita 80.

Har ila yau Rauhani ya kara da cewa muna sanarwa da Amurka,a yau muna cikin kasahen masu diinbin arzikiduk da adawa da takunkunmin zalunci da ta kakabawa Iran, yanzu kamfanonin mai da ma’aikata da injinoyoyinta sun yi nasarar gano wani katafaren fili mai cikin da danyen man fetur.

Daga karshe shugaban Rauhani ya jaddada cewa mun yi nasarar ne sakamkon jajircewa da tsayin daka kan duk wani matsin lamba da takunkumin Amurka da sauran kawayenta na turai na tsawon shekara guda, a daidai lokacin da mutanen mu sauke cikin matsanancin hali.