Idan akwai wani batu da aka tayar da kura a makon nan, shi ne na tashin Shugaba Muhammadu Buhari zuwa kasar Saudiyya domin halartar wani taron kasuwanci, inda daga nan zai wuce zuwa birnin Landan, kafin daga bisani ya koma Najeriya a ranar 17 ga Nuwamba.

A ranar Asabar din nan ne ake sa ran Shugaba Buharin zai bar kasar Saudiyya zuwa Birtaniya domin kai wata ziyarar radin-kai inda zai kwashe kwana 17.

Idan har Buhari ya koma Najeriya a ranar 17 ga watan Nuwamba, to lissafi zai kama kwanaki 425 ke nan shugaban ya yi a kasashen waje a tsawon shekara hudu da rabi na mulkinsa.

 Kaduna press  ta duba kundinta tare da samun karin wasu bayanai daga jaridar Daily Trust dangane da kwanakin da shugaban ya yi a wajen Najeriya, kamar haka:

2015
3 Yuni - Niamey - Niger - Taron koli kan Boko Haram (tafiyar Buhari kasar waje mako guda bayan shan rantsuwa)
4 Yuni - N'Djamena - Chad - Ziyarar aiki
7 - 8 Yuni - Munich - Germany - Taron koli na kasashen G7 na 42
12 - 13 Yuni - Johannesburg - Afirka ta Kudu - Taron Tarayyar Afirka na 25
19 - 23 Yuli - Washington, D.C. - Amurka - Ziyarar aiki
29 - 30 Yuli - Yaoundé - Cameroon - Ziyarar aiki
2 - 3 Agusta - Cotonou - Benin - Bikin 'yancin kai
7 Satumba - Accra - Ghana - Ziyarar aiki
14 - 16 Satumba - Paris- Faransa - Ziyarar aiki
24 - 29 Satumba - New York City - Amurka - Babban taron Majalisar DInkin Duniya na 70
26 - 30 Oktoba - New Delhi - India - Taron koli na India da Afirka na uku
30 Oktoba - Khartoum - Sudan - Ziyarar aiki
22 - 24 Nuwamba - Tehran - Iran - Taron kasashe masu fitar da iskar Gas na uku
28 - 30 Nuwamba - Valletta - Malta - Taron kasashe rainon Ingila na 2015
30 Nuwamba - 1 Disamba - Paris - Faransa - Taron kungiyoyin Paris na 21
4 - 5 Disamba - Johannesburg - South Africa - Taron koli na China da Afirka
10 December -Benin Republic - Jana'izar Shugaba Mathieu Kerekou

2016
8 Janairu - Benin- Cotonou - Taron koli na Shugabannin kasashen da ke kewaye da ruwan Nijar kaso na 11
17 - 20 Janairi - Abu Dhabi - Dubai - Taron koli kan makamashi
26 Janairu - Addis Ababa - Ethiopia - Taron shugabannin kasashen Tarayyar Afirka na 26.
27 - 29 Janairu - Eldoret, Nairobi - Kenya - Ziyarar aiki.
2 - 4 Fabrairu - Strasbourg - Faransa - Ziyarar aiki
5 - 10 Fabrairu - London - Birtaniya - Hutu
18 Fabrairu - Sharm El Sheikh - Egypt - Taron Afirka na 2016'
22 - 27 Fabrairu - Riyadh, Jiddah, Makka, Madina - Saudiyya - Ziyarar aiki
27 - 28 Fabrairu - Doha- Qatar- Taron Kungiyar OPEC
14 Maris - Malabo - Equatorial Guinea - Ziyarar aiki
30 Maris - 3 Afrilu - Washington, D.C. - Amurka - Taron koli kan nukiliya na 4
11 - 14 Afrilu - Beijing - China - Ziyarar aiki
13 Mayu - 15 Mayu - London - Birtaniya - Taron koli kan rashawa da cin hanci
6 - 19 Yuni - London - Birtaniya - Jinyar rashin lafiya
8 Agusta - N'Djamena - Chad - Rantsar da Shugaba Idris Deby
27 - 28 Agusta - Nairobi - Kenya - Taron Tokyo kan Afirka
13 - 16 Oktoba - Berlin - Jamus - Ziyarar aiki
14 - 18 Nuwamba - Marrakesh - Morocco - Taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi
22 Nuwamba - Equitorial Guinea - Taron kasashen Afirka da na Larabawa karo na hudu
5 - 7 Disamba - Dakar - Senegal - Taron kasashen duniya kan zaman lafiya da tsaro a Afirka
13 Disamba - Banjul - Gambia - Taron koli na ECOWAS

2017
7 Janairu - Accra - Ghana - Rantsar da Shugaba Nana Akufo-Addo
12 Janairu - Banjul - Gambia - Taron sulhu na ECOWAS
13 - 14 Janairu - Bamako - Mali - Taron koli tsakanin Afirka da Faransa
19 Janairu - 30 Maris - Landan - Birtaniya - Hutu da jinya
7 Mayu - 13 August - Landon - Jinya
17-21 Satumba - Amurka - Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 72
21- 25 Satumba - London - Birtaniya - Hutu
18 - 22 Oktoba - Santambul - Turkiyya - Ziyarar aiki da taron kasashe takwas masu tasowa
24 Oktoba -Yamai - Jamhuriyar Nijar - Taro kan samar da kudin bai daya na kungiyar ECOWAS
28 Nuwamba - Abidjan, Cote d'voire - taron Tarayyar Afirka da Tarayyar Turai karo na biyar.
11 Disam