Dangane da kammala Digirinta na biyu (MSc) a fannin ilimin Nanotechnology a jami'ar Tehran (TUMS).

*(MSc in Medical Nanotechnology)*

Yau aka yi musu Walimar kammalawa.
Wani abin farin ciki shine, Course din Nanotechnology, duk da yadda ake ji da shi a duniya, amma bakon ilimi ne a wajen Yan Nijeriya, kusan ita ce mutum na farko a kaf kasar nan da ya fara yinsa, saura za su biyo baya.

Allah Ya ba da sa'a a abin da ya rage na karatun. Ya kara himma da kwazo da damar cigaba.

Ya kuma amfanar da al'umma da Harkar Musulunci da ilimin nasu.

Allah ya gaggauta bayyanar mana da Sheikh Muktar Sahabi Tare da sauran yan uwan mu.