Rahotannin sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Al’hilal da ke wakiltar kasar Saudiyya a gasar kwallon kafa na cin kofin zakarun club din Asiya, ta zama zakara bayan da ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta kasar Japan da ci 2-0 a wasan karshe wato final da suka buga.

Wannan shi ne karo na 3 da kungiyar kwallon kafa ta Al’hilal ta kasar Saudiyya ta dauke kofi , inda ta taba dauke kofin har sau biyu a baya a shekarun 1992 da kuma 2000.

A gefe guda kuma kasar Ivory coast ta lallasa kasarRwanda da ci 6, Rwandan kuma tana da 3 a gasar kwallon zari ruga wato Rugby. 

yanzu kasar Ivory coast ta shiga mataki na gaba a wasannin neman gurbi a gasar kallon Rogby na cin kofin Afrika da za’a yi a shekara mai zuwa ta 2020, inda za ta fuskanci Kenya da moroko. Ita ma kasar Ghana haka lamarin yake bayan da ta lallasa Botswana da ci 36-25kuma zata kara da Tunisiya da Zimbabwe a nan gaba.