A ci gaba da gwagwarmayar da kungiyar kwadago ta kasa a Nigeria ta ke yi na ganin an fara aiki da sabon tsarin biyan mafi karancin albashi a fadin kasa baki daya, kungiyar ta bukaci yan majalisun jahohi da su bayar da hadin kai wajen matsin lamba ga gamnonin jahohinsu da su fara biyan mafi karancin albashi na N30,000.

Da yake bayani ga manema labarai a jihar Legos sakataren kungiyar kwadago ta kasaMr Emannuel Ugboaja ya shawarciyan majalisun jahohinda su tsige duk gwamnan da ya kibiyan mafi karancin albashin.

Wannan yana zuwa ne bayan da kungiyar gwamnoni ta kasar NGF ta fitar da wata sanarwa a wani taro da gwamnonin suka yi , inda suka bayyana cewa gwamnonin ba za su biya abin da ya fi karfin abin da suke samu ba, kuma matakin da gwamnatin tarayyar ta dauka na amincewa da fara biyan mafi karancin albashi bai shafisauran johohin kasar ba.