shirya kuma ta gabatar da bikin Mauludin Manzon Allah (s) a harabar makarantar dake layin turaki by PRP road Rigasa Kaduna.

Wakilin 'yan uwa na da'irar Kaduna Sheikh Aliyu Tirmidhiy ne babban bako, wanda ya gabatar da jawabi a muhallin taron,
Shehin malamin yayi jawabai masu ratsa jikin gaske, ta yadda ya tabo janibobi daban-daban akan al'amarin mauludin na Ma'aiki,
Sheikh Aliyu yayi bayanai akan muhimman abubuwa guda uku a bisa rayuwar Manzon Allah, ta yadda ya fara tabo tarihin haihuwarsa da rayuwarsa, a matsayin abu na farko,
Malamin ya bayyana yadda'aka haifi fiyayyen halitta (s) da irin abubuwan al'ajabobin da suka faru lokacin haihuwarsa, kamar mutuwar wuta wacce aka shekara dari hudu ana izata, da faduwar katangun kisira, da kuma faduwar gumaka, da ire-iren aja'ib da mahaifiyarsa (S) ta gani kuma taji.
Haka zalika Malamin yayi dugon bayani akan irin mu'ujizozin da Allah (T) ya baiwa shi Manzon, babbar mu'ujizarsa a shine Alqur'ani mai girma, injishi, acikinsa Allah yana cewa "WASSHAMSU TAJZIY LI MUSTAQARRUN LAHA......." Wani daga cikin masu ilimin kimiyya yake fadin cewa lallai akwai wani babban lamari game da wannan mutumi (S.A.W), domin tayaya yasan cewa rana tana jujjuyawane kuma a lokacinsa babu microscope ko wani abu makamancin haka, lallai akwai wanda yake sanar dashi hakan (bayan sunyi bincike sun gano yadda rana ke juyawa, aka fadi musu gashi acikin Alqur'ani).
Akarshe Malamin yayi bayani a bisa kyawawan dabi'u irin nashi
(MUKHARIMUL AKHLAQ), Malamin yayi bayanai masu gamsarwa a bisa kyawawan dabi'un nasa, bayan da aka rushe ka'aba kafin aikoshi da Annabta sai kabilun larabawa suka taru domin mayar da dutsen na ka'aba, suna jayayya akan kowa nason shine zai mayar da dutsen, a karshe sukayi ittifakin duk wanda ya fara zuwa gurin ta bangare kaza shine zai mayar, sai ko ga Ma'aiki nan ta bangaren ko wannensu suna fadin cewa mun yarda da Al'ameen, a karsheMa'aiki ya mayar musu da Dutsen, kaga kyawawan dami'unsa ne ya janyo hakan, inji Malamin.
Malamin bai karkare ba saida ya shaidawa mahalarta taron cewa lallai fa'idantuwa da Mauludi ba shine kawai azo ayi bikin Maulud aci abinci asha abinsha kawai a tashi ba shikenan, a'a fa'idan shine mu dauki dukkanin rayuwarSA (S.A.W) mu aikatashi a aikace, muyi iyakacin kokarinmu na ganin munyi koyi da duk rayuwarsa (S.A.W).

Bayan jawabinsa sai pastor Yohana D.Y Buru ya gabatar da jawabi akan muhimmancin neman ilimi ga matasa.
Pastor yayi jawabai masu muhimmancin gaske kuma masu ratsa jiki sosan gaske, neman ilimi bai takaitu ga iyakacin na boko ba kawai a'a dole mutum ya nemi ilimin addininsa, a cikin ilimin addininka ne zaka san Ubangijinka sannan da yadda zakayi masa biyayya da bauta masa, a matsayinku na Musulmai ya kamata ku sani cewa Annabi Muhammad yazo ne domin ya kawar da jahilci, don haka wajibine gareku musamman matasa ku nemi ilimi, kuyi karatu, inji shi.
Malam Zakzakiy ya taba fada min cewa pastor kada ka kuskura ka shiga addinin da baka da ilimi akanshi, karka shiga abinda kake da jahilci akansa (harda addinin da nike fa na kirita), inji Pastor.

A karshe aka gayyato principal din makarantar Malam Abdul Buhari domin yayi karin bayanai akan makarantar.
Malamin ya shaidawa mahalartan yadda suka fara karatu tun farko, inda a karshe ya bayyana cewa zuwa yanzu suna yin diploma a bangaren Environmental Health da kuma Dental Health ba'ada bayan first aids da sukeyi, kuma sun samu damar hada hannu da wasu makarantu domin yin aiki kafada-da-kafada don samarwa da daliban makarantar abubuwan da suke da bukata.
A karshe akayi Addu'a aka sallami kowa.

-KNPRSCD 06.
-Kaduna Press.
-Jabeer Bin Said Al'ansariy.