Kamar Yadda muke gani a hotuna, Wakilin 'Yan uwa na Katsina Shaikh Yaqub Yahya ya amsa goron gayyatar Makwabtansa zuwa Mauludin Fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S).

Mauludin da Makarantar Shehu Mani Suka shirya ya samu halartar Mutane da dama da Malamai da dama wadanda sukayi jawabai, sannan aka ba shaikh Yaqub dama yayi jawabinsa. Jawabin Shaikh Yaqub ya saka mahalartan natsuwa da sauraronshi Wanda Kai da ganin fuskoki, gami da natsuwar Mahalartan kasan jawabin Shaihin Malamin ya ratsasu.

A jawabin Malam ya tabo irin yadda Gwamnati (yahudawa) ke ta kokarin sai sun rusa addini ta kowane bangare shiyasa suke ta rara gefe, yau su tabo can gobe su tsakulo Nan kokarinsu dai suga sun dakushe da kassara addinin islama. Shaikh ya nuna irin yadda ake kokarin yaki da makarantun Allo ta yadda aka fara da gidajen Mari (Malam Niga), yace; to ba nan suke nufi  ba a'a ilimin addininmu musamma Alqur'ani mai girma shi suke hari, yadda za'a wayi gari ko liman ba za'a samu ba Mai ilimin da zai ja sallah saboda ba ilimin Alqur'ani.

Wannan Mauludin anyi shi Ne A great Ranar Asabar da dare, 02/11/2019, A unguwar Sauri ba wurin zuwa Makarantar Shehu Mani Katsina.

Barka Da Maulud