Majalisar dattawan Najeriya ta gabatar da wani kudiri kan daukar matakan ladabtarwa a kan masu aikata barna ta hanyar kafofin sadarwa na zamani.

Jaridar Daily Trust  a Najeriya ta bayar da rahoton cewa, Majalisar Dattawan Najeriya ta sake dawo da kudirin da zai tsaftace Kafafen Sadarwar Zamani a kasar,.
Wannan kudirin dokar zai tanadar da daurin shekara uku a gidan yari ga duk wanda taka dokar ta aka gindaya.

A cewar Majalisar wannan kudiri zai taimaka wajen yakar yada labaran karya a shafukan yanar gizo da shafukan sada zumunta a Najeriya.

An dai gabatar da wannan kudiri a zauren majalisar ne da nufin hana yada labaran karya wadanda za su iya haddasa matsaloli a cikin kasa, ko kuma kawo rashin jituwa a tsakanin al’umma.