ke son ganin an rusa tsarin rayuwarmu baki daya domin yin gyara."
Toshon shugaban Amurka Barack Obama ya gargadi 'yan jam'iyyarsa ta Democrat masu neman tsayawa takarar mukamin shugaban kasa, ya nemi su yi hattara kan rungumar tsare-tsaren da a zahiri ba masu yiwuwa ba ne.

Mista Obama ya ce 'yan Democrat na iya raba gari da masu zabe idan suka ci gaba da karkata bangaren masu ra'ayin rikau a siyasance.

Tsohon shugaban na magana ne yayin wani taron tara kudade domin zaben shekara ta 2020, kuma ya ce yawancin masu zabe ba sa son ganin, "an rusa tsarin rayuwarmu baki daya domin yin gyara."

TALLA

Kawo yanzu Mista Obama bai bayyana dan takarar da yake mara wa baya ba.

A halin yanzu akwai 'yan takara 18 da ke neman zama wanda jam'iyyar ta Democrat za ta tsayar a matsayin dan takarar da zai kalubalanci Shugaba Donald Trump a zaben shugaban kasa na 2020.

Hillary Clinton ta ce an matsa mata ta tsaya takara 2020
Mai kudin duniya zai yi takara da Donald Trump
Wadanda ke kan gaba a halin yanzu su ne tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, da Sanata Elizabeth Warren da Sanata Bernie Sanders da kuma Pete Buttigieg, wanda shi ne magajin garin South Bend na jihar Indiana.Barack Obama tare da tsohon mataimakinsa Joe Biden a 2008, lokacin suna kan mulki
Wane ne zai kara da Trump a 2020?

Saura kasa da shekara guda a gudanar da zaben shugaban Amurka, kuma 'yan jam'iyyar Democrat na ta kokarin fitar da dan takarar da zai ja daga da shi.

Alkaluma na baya-bayan nan na nuna Joe Biden da Elizabeth Warren da Bernie sanders da kuma Pete Buttigieg ne ke kan gaba cikin masu neman mukamin su 18.

Labarai bags
Kaduna press