Kungiyar PIJ ta sha alwashin daukar fansa kan mutuwar Abu al-Ata
Wani harin sama da Isra'ila ta kai Zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar wani babban kwamandan kungiyar mayaka masu fafutukar jihadi ta Falasdinawa PIJ.

Baha Abu al-Ata ya mutu tare da matarsa a lokacin da makami mai linzami ya fada gidansu, a cewar kungiyar. Rahotanni sun ce hudu daga cikin 'ya'yansu da kuma wani makwabcinsu sun ji rauni.

Firai ministan Isra'ila ya ce reshe ne ya so juyewa da mujiya don Abu al-Ata dama yana shirin kai hare-hare Isra'ilan.

TALLA

A kalla rokoki 150 aka harba Isra'ila daga Gaza tun bayan kisan, wacce kungiyar ta PIJ ta sha alwashin daukar fansa.


Ku kalli bidiyon yadda aka harba roka daga Zirin Gaza zuwa Isra'ila
'Yan Isra'ila 17 ne hare-haren rokokin suka ji wa rauni a kudanci, a cewar Cibiyar Lafiya Ta Barzilai Medical Center da ke birnin Ashkelon.

Ma'aikatan lafiya sun ce an kuma ji wa wata yarinya mai shekara takwas rauni kuma tana cikin tsananin hali bayan da ta fadi magashiyyan a yayin da iyayenta suka ruga wani waje don fakewa, lokacin da suka ji karar harba harin sama a Holon da ke kudancin Tel Aviv.

A kuma daidai lokacin da aka kai wa Abu al-Ata hari ne wasu mutum biyun suka mutu aka kuma ji wa mutum 10 rauni a wani harin sama da aka kai gidan wani dan kungiyar ta PIJ a birnin Damascus na Syria, a cewar kamfanin dillancin labaran Syria, Sana.


Kafofin yada labaran Syrian sun ce wani harin saman Isra'ila ya sake fadawa gidan wani dan kungiyar PIJ a Damascus
Kafar yada labaran Sana ta ambato cewa jagoran kungiyar PIJ Akram al-Ajouri, bai samu rauni ba amma dansa na daga cikin wadanda suka rasu. Amma sojin Isra'ila ba su ce uffan ba kan batun.

Hedikwatar kungiyar PIJ, wadda ke samun goyon bayan kasar Iran dai a birnin Damascus take, kuma daya ce daga cikin kugiyoyi masu karfi a zirin Gaza.

Shin me ya faru a Gaza?

Jiragen yakin Isra'ila su ne suka harba makamai masu linzami a wata unguwa da ke yammacin yankin Sheijaiya da ke Gaza da safiyar Talata, lamarin da ya haifar da tashin bama-bamai ana kuma iya hango yadda wuta ta tashi a wurin a nisan kilomita daga wurin.

Makami mai linzamin ya fada kan wani dogon gini inda ya lalata hawa na uku na gidan, ya kuma hallaka Abu al-Ata Ida mai dakinsa.

KNPRSCD 08
Kaduna press