Yanzu wata biyu ke nan da Najeriya, daya daga cikin manyan kashen Afirka ta rufe dukkan iyakokinta na kan tudu domin dakile ayyukan fasa-kwauri. Sai dai kuma matakin wanda ba'a taba ganin irin sa ba, na kawo cikas ga harkokin kasuwanci a yankin.

Iyakokin kasar wadanda a baya suke cike da hada-hada, yanzu sun tsaya cik. Baya ga kayayyaki da ke rubewa da dogon layin manyan motoci a shingayen bincike da ke jiran a sake bude iyakokin kasar.
A ranar 21 ga watan Agusta ne Najeriya ta rufe iyakokinta na kan tudu ba tare da wani gargadi ba - abin da ya fusata kasashe masu makwabtaka da ita.

Me ya sa aka dauki matakin?
Babban abin da ya sa Najeriya ta dauki matakin shi ne shinkafa. Kasar na takaicin yadda ake ta karya dokar da ta sanya na haramta shigo da shinkafa ta iyakonkinta na kan tudu.

Masu fasa-kwaurin shinkafa daga Jamhuriyar Benin na samun riba sosai.
Babbar haramtacciyar hanyar da suke bi na tsakanin Cotonou, birni mafi girma a Jamhuriyar Benin da kuma Legas, babban birnin kasuwancin Najeriya, mai nisan tafiyar 'yan sa'o'i.

Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Jamhuriyar Benin ya dogara ne sosai a kan sake fitar da kaya da harkar fiton kayan zuwa Najeriya. Bangaren na samar da kusan kashi 20 na kudaden shigar kasar.
Bankin ya kara da cewa kashi 80 na kayan da ake shigar da su Jamhuriyar Benin, akan saye su ne domin kaiwa Najeriya.
A 2004 Najeriya ta haramta shigar da shinkafa daga Jamhuriyar Benin, kafin a 2016 ta haramta shigo da shinkafar daga dukkan sauran makwabtanta. Amma duk da haka ba'a daina shigo da shinkafa kasar daga ketare ba.

Me ya sa shinkafa ke da riba sosai?
Ta tashoshin ruwa ne kadai Najeriya ta amince a shigo da shinkafa kasar. Tun a 2013 kasar ta sanya harajin kashi 70% a kan shinkafar da aka shigo da ita ta tashoshin ruwan.

Manufar matakin shi ne ba wa manoman shinkafa a kasar kwarin gwiwa, baya ga neman kara yawan kudaden shiga.
Sai dai kuma 'yan fasa-kwauri na amfani da damar saukin shigowa da shinkafa ta kasashe masu makwaftaka.
Shafin harkar teku ta Najeriya 'Ships and Ports' ya ce a 2014 Jamhuriyar Benin ta rage harajin da take karba a kan shinkafar dake shiga kasar daga kashi 35 na farashin da aka saye ta zuwa kashi 7. Ita kuma kamaru ta soke harajin kashi 10 da take karba a kan shinkafa 'yar waje.

Rice import from Thailand (metric tonnes)