Sayyid Badamasi Yaqub Ya Jagorancin kai ta'aziyya ga iyalan marigayi Sheikh Dawood a madadin harkar musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibrahim yaqub Zakzaky (h),  Onyebuchi a garin Owere jihar Imo.

Ziyarar wacce ta hada da Sayyid Badamasi Yaqub, tare da yan rakiyar sa Sheikh Muhammad Abbari, Sheikh Abbakar (Abu-Sumayyah), da Sheikh Rabiu Funtua, Sheikh Abubakar A A, Bugawa.
Sun isar da saƙon ta'aziyar ga ilayalan Sheikh Dawud Onyabucha na wannan babbar rashin da mukayi, da Addu'oi na musamman ga shi mamacin, da karfafa iyalansa a kan turban da ya basu a kai.

Sun sami ganawa da babban dan sheikh dawud, da sauran iyalai, 

Hakanan wakilin sarkin hausawan Owere shima ya gana  da su Sayyid din,

Muna addu'a Allah ya haskaka kabarin Sheikh Dawud Onyabucha ya kuma albarkaci zuriyarsa.