Mohammad Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar hako mai a doron kasa da kuma cikin teku, wanda haka zai kara yawan kudaden da kasar take samu daga man da ake hakowa daga rijiyoyin mai cikin teku da kuma doron kasa.

Kuma tun makwanni biyu da suka gabata ne majalisar dattawa ta kasar ta amince da kudurin kafin daga bisani a dowa da ita gashugaban kasa ya sanya hannu domin ta zama doka.

Wannan yana zuwa ne adaida lokacin da babban Antoney Janar din kasar kuma minsitan shari’a Abubakar Malami ya fara wani yunkuri na ganin an dawo da tsabar kudi har dala biliyan 62 daga kamfanonin mai na kasashen waje da suka kunshi kudaden ariyas na haraji da ya kamata su ba wa Nigeria natsawon shekaru da suka gabata tun lokacin ana sayar da mai akan dala 20 kan kowacce gangar mai.

A wani sako da ya aikeda shi ashafinsa na Twitter Muhammar Buhari ya fadi cewa yau na sanya hannu kan sabuwar doka da ya shafi hako mai a rijiyoin dake doron kasa da kuma cikin teku , yanzu Nigeria za ta samu cikakkenrabonta na kudaden shiga da ya kamata ta samu daga albarkatun kasa da Allah ya ba taa karon farko tun daga shekara ta 2003.