Shugaban kasar Bolivia Evo Morales ya bada sanarwan sauka daga kujerar shugabancin kasar a jiya Lahadi. Morales wanda ya share shekaru 14 yana jagorancin kasar Bolivia ba tare da neman tallafin manya-manyan cibiyoyin kudade na duniya ba ya sauka daga Mukaminsa a jiya Lahadi.

Evo Morales ya kyautata tattalin arzikin kasar ta Bolivia a cikin shekaru kimani 14 da yayi yana jagorantar kasar. Amma kasashen yamma musamman Amurka sun ci gaba da bawa masu bore a kasar goyon baya a cikin makonni uku da suka gabata wanda ya tilasta Evo Morales ajiye aikinsa na shugabancin kasar a jiya Lahadi.

Morales ya hau kan kujerar shugabancin kasar ta Bolivia ne a shekara ta 2006, kuma a zaben ranar 20 ga watan Octoba na wannan shekara aka gudanar da zabubbuka inda ya sami karamin rinjaye a kan abokin hamayyarsa a zaben, wanda ya bashi damar fara shugabancinsa wa’adi na hudu.