Kawo yanzu babu rahotonnin kungiyar Hamas da ke iko da Gaza ta shiga wannan fada. Wakiliyarmu Kaduna press Barbara Plett Usher da ke Kudus ta ce matukar suka shiga lamarin zai kara kazancewa.

A kokarin kaucewa hakan, jami'ai a Isra'ila sun maida hankali kan kai wa mayakan PIJ hari, tare da kaucewa duk abin da zai gifta tsakaninsu da Hamas.

Masu aiko da rahotanni sun ce wannan ne karon farko da jami'an Isra'ila ke shata layi tsakaninsu da Hamas tare da kaffa-kaffa dan kar wani sabani ya shiga tsakaninsu.

A baya an saba ganin yadda Isra'ila ke dora alhakin abubuwa da dama kan kungiyar Hamas wadda ke iko da Gaza.

KNPRSCD 08
Kaduna press