amfani da su na neman karfin fada a ji fiye da abokiyar hamayyarta Saudiyya a yankin Gabas Ta Tsakiya, kamar yadda wani bincike da wata cibiyar bincike ta kasa da kasa da ke Birtaniya, International Institute for Strategic Studies (IISS) ya nuna.

Abokan hamayyar Iran na yankin sun kashe biliyoyin daloliya wajen sayen makamai daga kasashen yamma, kuma mafi yawa daga Burtaniya suka saya.

Duk da wannan makudan kudi da ake kashewa, Iran wacce aka kakabawa takunkumai ta samu nasarar karuwar tasiri a bangarori masu muhimmanci a yankin Gabas Ta Tsakiya.

TALLA

Tana da karfin fada a ji - wanda ya samo asali ta hanyar samun damar iko a wasu lamuran da suka hada da abin da ya shafi Syria da Lebanon da Iraki da kuma Yemen.

'Cusa ra'ayi'

Sai dai kafa kungiyoyin da Iran take yi na 'yan tawaye a fadin Gabas Ta Tsakiya, wadanda suke taya ta yaki da gwamnatocin yankin ba sabon abu ba ne.

Tun bayan da kasar ta fara kafa Kungiyar Hezbollah a Lebanon, sai take ta neman yadda za ta dinga cusa ra'ayinta na juyin juya hali ga wasu kasashen da kuma fadada tasirinta a sauran wurare tun bayan komawar Ayatollah Ruhollah Khomeini Tehran a shekarar 1979.

Amma rahoton Cibiyar IISS mai shafi 217, mai taken "Iran's Networks of Influence in the Middle East", (Tasirin Iran a yankin Gabas ta Tsakiya), ya samar da bayanan da ba su taba bayyana ba kan ayyukan da Iran ke yi a yankin.

Rahoton ya ce, "Jamhuriyyar Musulunci ta Iran ta karkato da hankulan kasashen duniya kanta a matsayin kasa mai karfin fada a ji a yankin Gabas Ta Tsakiya."

Mawallafan sun kuma ce: "Ta samu wannan nasara ce ta hanyar kalubalantar manyan kasashe da tasiri kan wasu aikace-aikacenta da kuma amfani da wasu dabaru na bayan gida."

Abu mafi muhimmanci a nan shi ne amfani da wata runduna ta dakarun juyin juya hali na kasar Iran da ke aiki a kasashen waje IRGC.

Da dakarun juyin juya halin da shugabansu Manjo Janar Qasem Soleimani suna aiki ne karkashin umarnin jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamanei, wanda hakan ya sa suka kauce wa tsarin gudanarwa na rundunar sojin kasar da hakan ya sa suka zama wani bangare mai cin gashin kansa.


KNPRSCD 08
Kaduna press
Safuwan Sp harun✍🏻