Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

TEHRAN: YAU MILIYOYIN MUTANE SUN FITO KAN TITUNAR BIRNIN TEHRAN DOMIN YIN ZANGA ZANGAR GOYON BAYAN JUMHURIYAR MUSULUNCI....Da yake jawabi a wajen gangamin kwamandar rundunar IRGC Manjo Janar Husaini Salami ya bayyana Cewar "Iran ta sake marin Amurka da kawayenta a fuska,sun ta kasa yin komai.

Yace yau shekara 40 kenan Amurka na shirya mana kutungwila,amma har yau babu nasara ko da kwaya daya da ta samu.

Yace,da Amurka,Faransa,Burtaniya da Saudia sun gada karfinsu kan Iran,amma a karshe mun dalla musu mari a fuakarsu,kuma sun kasa ramawa.

Yace sun kwashe shekaru suna yin tanadi,amma cikin kasa da awa 48 mun kawo karshen mafarkinsu na shekaru.
Kuma ko gobe suka sake shiryawa suka zo to zasu karke ne a kurkuku,tare da karbar hukunci mai gauni.

Muna fada musu Cewar,muna da hakuri,amma hakurin namu yana da iyaka. Don haka yakamata su mutunta al'ummar Iran inji Janaral Salami Yace wadanda suka kasa daukar marakin soja a kan mu,ta yaya zasu yi nasara ta hanyar yin amfani da yan daba??

Post a Comment

0 Comments

Close Menu