Sharadi na uku    Shi ma wannan sharadin dole ne cewa a yi wa kayayyakin da za a shigo da su daga makwabtan kasashe rakiya.   

Dole masu rakiyar su taso tare da kayayyakin tun daga wata tashar jiragen ruwa da ke yankin, kai tsaye zuwa bakin iyakar Najeriya.   

Sharadi na hudu Haka kuma mutanen da ke da fasfo ne kawai za a bari su ketaro cikin kasar.

Onyema ya yi gargadin cewa, kasar ba za ta amince da wata takarda ko katin shaidar zama dan kasa ba.

Nan da makonni biyu masu zuwa ne ake sa ran wani kwamiti wanda ya kunshi wakilai daga kasashen Benin da jamhuriyyar Niger da kuma Najeriyar zasu gana.

Ministocin kudi da na harkokin waje da na cikin gida da shugabannin hukumomin hana fasakauri da na shige da fice da hukumomin tattara bayanan sirri na kasashen ne za su yi wannan ganawar. In ji Mista Onyeama.