A yau ne a ka dawo katu dan cigaba da sauraron shari'ar yan uwa Almajiran Malam Zakzaky wanda da a ke tsare da su tin aika aikan sojojin Najeriya a a ranar 12-12-2015 a zaria.

Idan mai karatu bai manta ba ana tsare da wadan nan bayin Allah ne tin ranar 12-12-2015, bayan afkawar da sojojin Najeriya tayi ma Sheikh Zakzaky da Almajiransa, yayin da suka kashe sama da dubu (1000+) da da yayan shi uku, da kona yayar sa da ranta. Da tsare shi da iyalan sa, da daruruwan almajiran sa.

Amma abin mamaki a nan shi ne: ba a kallon duk wannan nuna fin karfin da take hakkin a matsayin laifi, wai a na tuhumar su da kashe soja daya, da cikin Makasan su.

Yayin da a ka kwashe shekaru a na yawo da hankalin mutane, ba tare da wani cikekken hujja ba, da sunan shari'a.

To yau ma kamar kullum sun yi abin da suka saba, bayan isowar yan wa da a ke zargi kotu, mun dauki kusan awa biyu muna jiran isowar lauyoyi da Alkalai, isowar su ke da wuya sai wulakancin jami’an tsaron prison yead da na yan sandan ya tashi, yayin da suka fara Koran jama'a da karan su, haka dai mukayi hakuri da wannan wulakancin dan, kasancewa  a wajen.

Lauyoyin da ga duka janibin sun gabatar da kan su, dan cigaba da wannan shari'a, sai mai wakiltar bangaren gwamnatin bayaro dari, yace ba a bashi takardar shaida na hujjojin, wadan da a ke zargin, yayin da mai wakiltar wadanda a ke zargi Maxiwel ya karya ta shi, ya ce ya bashi takardar hanu da hannu.

Sai mai shari'a ta ce: ta daga shari'ar zuwa ranar 18 ga watan 12, yayin da bayaro dari ya mike yace yana da shari’a a wannan ranar, sai a ka mai da shi zuwa ranar 19th ga watan 12, (12-12-2019).

Allah zai cika hasken sa ko da kafurai da munafukai sun ki.

KNPRSCD 07 ✍️
KADUNA PRESS