Ministan shari’a na kasar Najeriya Malam Abubakar Malami ne ya bayyana cewa; Ya bayar da umarni ga hukumar jami’an tsaro ta farin kaya, DSS, akan su saki tsohon mai bayar da shawara kan harkokin tsaron kasa, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya da kuma mr. Omoyele Sowore.

Jaridar Punch wacce ta buga labarin ta ci gaba da cewa; Tuni an kammala cike dukkanin takardun da ake bukata domin sakin wadannan mutanen biyu daga cibiyar hukumar leken asirin cikin gida DSS a Abuja.

Tun a cikin watan Disamba na 2015 ne dai ake tsare da Dasuki, yayin da aka kama Sowore a farkon wannan watan na Disamba.