Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Al’ummar Yemen Na Da Karfin Tinkarar Makiyansu Da Kuma Yin Nasara


Ministan tsaron kasar Iran ya bayyana cewa sojojin kasar Yemen sun kai matsayin dogaro da kansu wajen samar da makaman da suke bukata sannan kuma suna da karfi da za su iya tinkarar makiyansu da kuma yin galaba a kansu.

Ministan tsaron na Iran Birgediya Janar Amir Hatami ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da sabon jakadan kasar Yemen a Iran, Ibrahim Mohammad Al-Dailami inda ya ce wadannan nasarori sun ba wa duniya mamaki kamar yadda dakarun kasar Iran suka ba wa duniya mamaki a lokacin kallafaffen yaki na shekaru 8 da tsohuwar gwamnatin Saddam ta Iraki ta kallafa wa Iran.

Janar Hatami ya kara da cewa a halin yanzu Yemen ta kai matsayin karfin da za ta iya kutsawa cikin sahun makiya da kuma kai hari kan makiya din har na tsawon kilomita sama da 1000 wanda hakan wani gagarumin ci gaba ne, sai dai kuma ya ce hanya guda ta magance rikicin kasar ta Yemen ita ce tattaunawa tsakanin ‘yan kasar da kuma cimma matsayar yadda za su gudanar da kasar su ba tare da tsoma bakin ‘yan waje ba.

Kasar Yemen din dai tana fuskantar hare-haren wuce gona da iri daga sojojin Saudiyya da kawayenta tun a shekara ta 2015 lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar dubban mutanen kasar, sai dai kuma a halin yanzu dakarun Yemen din sun fara mayar da martani mai kaushi da kasashe masu wuce gona da irin musamman Saudiyya lamarin da ya ke ci gaba da tilasta wa Saudiyya neman mafita da tattaunawa.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu