A Uganda a kalla mutane 12 ne aka rawaito cewa sun rasa rayukansu wata ambaliyar ruwan sama data abkawa yankin Bundibuyo a yammacin kasar.

Wata sanarwa da kungiyar agaji ta Red-cross a kasar, ta fitar, ta ce an kai gawarwakin mutane 12 a asibitin yankin.
Bayanai sun ce an shafe sama da sa’o’I 9 ana tabkla rowan sama a yankin tun daga ranar Juma’a.

Kawo yanzu ma’aikatan agaji da suka hada da jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da aikin ceto a yankin.

Yankin gabashin Afrika da kuma tsakiya na fama da matsalar ambaliyar rowan sama a baya bayan nan, wanda aka shafe gomman shekaru ba a taba ganin irinsa ba.