Cikin watani biyu da suka gabata ruwan sama kamar da bakin kwarya gami da ambaliyar ruwa ya yi sanadiyar kashe mutane 265 a kasashen gabashin Afirka
Tashar talabijin din France 24 ta habarta cewa cikin watani biyu da suka gabata, ruwan sama kamar da bakin kwarya gami da ambaliyar ruwa ya yi sanadiyar salwanta rayukan mutane akalla 265 da raba wasu dunban mutane da gidanjensu a kasashen Kenya da Burundi da Tanzaniya da Sudan ta kudu da Uganda gami da Habasha dake gabashin Afirka.

Rahoton ya ce a kasar Kenya kawai mutane 132 ne suka rasa rayukansu yayin da a kasar Burundi mutane 38.

A gabashin kasar kenya har yanzu ana ci gaba da neman gawawwakin mutane a cikin tabo duk kuwa da cewa da dama daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu a cikin tabon aka yi musu sutura.

A wasu yankunan dake kasar Sudan ta kudu wacce ta kwashe tsahon lokaci ta fama da matsalar yakin cikin gida, gidaje da wuraren noma ne ruwa ya mamaye, lamarin da ya sanya mutanen yakin suka nemi mafuka a sansanin kungiyoyin bayar da agaji.