Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Amurka Ta Bayyana Hanzarinta Kan Kakabawa Iran Takunkumi


Kakakin ma'aikatar harakokin wajen Amurka ya yi da'awar cewa Amurka ta kakabawa Iran takunkumi ne da nufin dawo da ita kan tebirin tattaunawa.

Tashar talabijin Aljazera ta kasar Qatar na nakalto kakakin ma'aikatar harakokin wajen Amurka Morgan Ortagus yayin da yake bayyana hamzarin kasarsa na kakabawa jamhoriyar musulinci ta Iran takunkumi mafi tsanani wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa ya ce Amurka ta yi hakan ne domin tilastawa kasar Iran din ta dawo kan tebirin tattaunawa, domin shugaba Trump na bayan cimma yarjejeniya mafi kyau, kuma Mu ko wani lokaci muna bayan warware matsaloli ta hanyar Diplomasiya.

Ortagus ya kara da cewa Amurka a shirye take da tattaunawa da kasar Iran amma hakan ba zai hana ta ci gaba da kakaba mata takunkumi mafi tsanani ba har zuwa lokacin da kasar Iran din za ta amince ta koma kan tebirin tattaunawa da Amurka.


Kakakin ma'aikatar harakokin wajen na Amurka ya ce a ganinsa siyasar matsin lamba kan kasar Iran na samun nasara, kuma kasashen Turai ma na son kasar Iran din ta canza salon siyasarsa.

A ranar 8 ga watan Mayu na shekarar 2018 din da ta gabata ce shugaba Donal Trump na Amurka ya fice daga cikin yarjejeniyar da Duniya ta cimma da kasar Iran kan shirin Nukiliyarta na zaman lafiya wanda kuma hakan ya sabawa dokokin kwamitin tsaro na MDD, tare kuma da sake kakabawa kasar ta Iran takunkumin ta'addanci na tattalin arziki.

Hukumomin birnin Tehran dai sun sha nanata cewa babu yadda za a yi sun koma tebirin tattauna cikin takumkumi da matsin lamba na kasar Amurkan.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu