Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Amurka Ta Gargadi Najeriya Akan Tauye Hakkin Yin Addini


A karon farko gwamnatin Amurika ta sanya Najeriya cikin kasashen da za ta sanya wa ido bisa zargin suna toye hakkin yin addinin da mutum ya ga dama.

Wannan na kunshe ne a rahoton shekara shekara da hukumar kare 'yancin yin addini ta Amurka ta fitar.

Amurka ta kuma caccaki mahukuntan Najeriya da kasa tabaka komai domin kare lafiyar fararen hula a daidai lokacin da kungiyoyin dake ikirari da sunan jihadi irinsu Boko Haram da ISWAP ke kashe fararen hula.

Rahoton ya kuma kalubalanci tsarewar da ake wa jagoran harkar musulinci a Najeriya ta (IMN) ta ‘yan shi’a cewa da Shaihk Ibrahim El-zakzaky da mai dakinsa da daruruwan mabiyansa, da kuma matakin da gwamnatin kasar na haramta harkar musulunci a najeriya baki daya.

Amurka dai ta ce zata sanya wa Najeriya da sauran kasashen dake da irin wannan zargin ido, amma idan suka gaza magance wannan matsala to kuwa zata kakaba musu takunkumin karayar tattalin arziki.

Rahoton ya kuma Ambato kasashe irinsu Saudiyya, Burma da China da Eritrea da Iran da Koriya ta Arewa da Pakistan da Tajikistan da kuma Turkmenistan a matsayin wandanda aka sake sanya sunayensu a jerin kasashen da ke take hakkin gudanar da addini.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu