Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Amurka Ta Ja Kunnen Najeriya Akan Sake Kame Sowore

Dan majalisar dattijan Amurka mai wakiltar New Jersye Bob Menendez ya yi tir da sake kamun da jami’an tsaron kasar ta Najeriya ( DSS) su ka yi wa Omoyele Sowore.

Dan majalisar na Amurka wanda ya gabatar da taron manema labaru a tare da mai dakin Sowore ya kuma ce; Muna sa ido muna bin diddigin abin da yake faruwa kuma za mu ci gaba da yin matsin lamba, sannan idan har wani abu ya faru da Sowore, to da akwai sakamako mai tsanani da zai biyo baya.

Jami’an tsaro na ciki ( DSS) sun sake kame Sowore ne dai jim kadan bayan da wata kotu ta yanke hukuncin a sake shi, lamarin da ya jawo suka daga cikin gida da waje.
Gabanin kamun nashi, Sowore ya taba rayuwa a kasar Amurka inda ya kafa jaridar nan ta shafin internet, Sahara Reporters.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu