Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Bukaci Hukunci Mai Tsauri Kan Wasu Tsaffin Jami’an Aljeriya


Ofishin mai shigar da kara na gwamnatin Aljeriya, ya bukaci hukucin zama gidan yari mai tsauri kan wasu tsaffin manyan jami’an gwamnatin kasar.

Daga cikinsu akwai tsafin firaministoci guda biyu na kasar ta Aljeriya, da suka hada da Ahmed Ouyahia da Abdelmalek Sellal wadanda aka bukaci yanke masu hukuncin zama gidan yari na shekaru ashirin, kan zarginsu da cin hanci da kuma karbar rashawa.

An kuma bukaci irin wannan hukuncin ga wani tsohon ministan ma’adanai na kasar dake da zama a ketare.

Ofishin mai shigar da kara ya kuma bukaci da’a kwace duk kaddarorin mutanen da kuma fitar da wani sammacin kame tsohon ministan na ma’adanai, saiddai lauyoyin mutanen da ake tuhumar na kauracewa zaman wanda suka ce ba adalci a ciki.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu