Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Cafke Bakin Haure Kusan 200 A Mauritania


Jami’an tsaron gabar ruwa a Mauritania, sun sanar da cafke bakin haure ‘yan asalin kasar Gambia su kimanin 200 dake kokarin isa turai ba bisa ka’ida ba, kwanaki biyu kacal bayan kifewar wani kwale kwale a gabar rowan wanda ya yi sanadin mutuwar bakin haure 63.

Hukumomin kasar sun ce ana tsare dab akin hauren su 192, kafin daga bisani a maida su kasarsu ta asali.

Kafin nan dai a cewar kamfanin dilancin labren AFP, bakin hauren na samun kula ta abinci da kuma abubuwa bukatuwa.
A ranar Labara data gabata bakin haure 63 ne suka rasa rayukansu a kokarin shiga turai bayan da kwale kwalen da suke ciki ya nutse.

Wasu alkalumman da Hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa cewa da (OIM), ta fitar sun ce bakin haure kimanin 25,000 ne suka rasa rayukansu tun daga watan janairu na 2014 a kokarin neman zuwa turai da zumar samun rayuwa mai inganci.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu