Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Cimma Yarjejeniyar Sufuri Tsakanin Kasashen Iran Da Oman


Ministan dake kula da harakokin hanya da gine-gine na kasar Iran tare da ministan masana'atu da kasuwanci na kasar Oman sun cimma yarjejeniya a bangaren sufuri na jiragen ruwa.

Rahoton ya ce bisa yarjejeniyar da aka cimma, kasashen biyu za su yi amfani da tashoshin ruwa na bangarorin biyu wajen sufurin kayayyakin kasuwanci da kuma musayar kayayyaki.

A cewar Muhamad Islami ministan dake kula da harakokin gine-gine da hanya na jamhoriyar musulinci ta Iran, kasashen biyu sun jima suna gudanar da harakokin kasuwanci a tsakaninsu cikin fahimtar juna, kamar yadda kuma a bangaren siyasa ma ba su da wata matsala, kafa kwamitin hadin gwiwa na kasuwanci tsakanin kasashen biyu wata dama ce na aiki tare a bangaren sufurin jiragen ruwa.

A nasa bangare Ministan masana'antu da kasuwanci na kasar Oman Ali bin Masoud al Sunaidy ya yi ishara kan kyakkyawar mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu, tare da nuna fatansa na ci gaba da bunkasa wannan alaka a fagage da dama.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu