Hukumar yaki da amfani da kwayoyi masu kara kuzari ta WADA ta amince da dakatar da kasar Rasha daga halartar wasannin Olympics da za’a yi a shekara ta 2020 a birnin Tokyo, da kuma gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya na shekara ta 2022 na tsawon shekaru 4, saboda rashin bayar da hadin kai da hukumar yaki da amfani da kwayoyi masu kara kuzari na kasar Rasha ta yi a lokacin bincike kan wasu yan wasan kasar ta Rasha.

A gefe guda kuma hukumar kwallon Criket ta Nigeria ta fitar da sunayen yan wasan da za su wakilce ta a gasar duniya ta cin kofin Criket ta yan kasa da shekaru 19 da za’a gudanar a kasar Afrika ta kudu daga ranar 20 zuwa 8 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa ta 2020.

Yan wasan sun kama hanyar zuwa kasar Afrika ta kudun ne domin fara shirye- shriye, inda za su buga wasannin sada zumunta da manyan kungiyoyin wasan Cricket na kasar domin shirya wa sosai na tunkarar gasar da za’a yi.