Rahotanni da suka fito daga kasar Algeria sun bayyana cewa: wata kutu ta daure wasu tsoffin fira ministoci guda biyu a gidan yari bayan da aka same su da laifin dake da dangantaka da cin hanci da rashawa. Daruruwan masu rajin kare Demkuradiya ne suka yi cincirindo a kofar Kotun da ke birnin Alges a yayin yanke hukumci kan Ahmed Ouyahia da kuma Abdulmalik Sellal.

Kotu ta daure Ouyahia ne na tsawon shekaru 15 a gidan yari, tare da cin sa tarar dala 16,000, yayin da shi kuma Sellal aka daureshi shekaru 12 a gidan yari da kuma cinsa tarar dala 8,000, kuma an zargesu ne da yin amfani da mukaminsu a almundahanar da aka yi a kamfanin kera motoci a kasar.

Sai dai wannan yana zuwa ne adaidai lokacin da daruruwan matasa a birnin na Alges suka gudanar da Zanga-zangar neman a kawo karshen mulkin tsoffi tare da ba wa matasa dama domin nuna tasu iyawar.a daidai lokacin da ake sa ran gudanar da zabubbuka a kasar wannan makon. Wani matashin ya bayyana cewa sabuwar gwamantin da za’a kafa ci gaban wadda ta gabace ta ne,tun da har yanzu tsoffin shuwagabannin su ne za su sake dawo wa matakin da mafiywancin alummar kasar suka yi watsi da shi.