Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF a takaice ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasan kwallon kafa da a cikinsu ne za’a zabi gwarzon dan kwallon kafar Afrika na shekara ta 2019, karo na 28,inda za’ayi la’akari da irin rawar da kowanne dan wasa ya ta ka a wasannin da ya buga a a wannan shekarar.

Jerin sunayen sun kunshi yan wasa 10 a bangaren maza sai kuma guda 5 a bangaren mata, sai kuma masu horar da yan wasa da kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Afrika da bangaren kulub-kulub da sauransu. kuma za’a sanar da gwarzon da ya daga tuta a lokacin bikin bada kyutar da za’a yi a ranar 7 ga watan Janairun shekara ta 2020, a kasar Masar.

A gefe daya kuma an bude gasar premier ta kasar Saliyo inda ya zo da wani sabon salo, wanda a karon farko an bude gasar da karanta take na musamman, kuma za’a sanya hoton kwallon da aka kawata da bajen gasar, da shafin yanar gizo da kuma logo a rigunan dukkan kungiyoyin kwallon kafa guda 14 da za su kara da juna a gasar.