Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Gano Runbum Makamman ‘Yan Ta’adda A Burkina Faso


Jami’an tsaron Jandarma a Burkina faso, sun gano wani makekin runbum makaman yakin ‘yan ta’adda a yankin Belhuro dake kuda da lardin Arbinda a arewacin kasar.

Jami’an sun gano makamman ne yayin da suke sintiri a yankin, kamar yadda wata majiyar tsaro ta shaidawa manema labarai.
A nata bangare rundinar sojin kasar ta Burkina Faso, ta ce an kashe ‘yan ta’adda hudu yayin samamen da suka kai kan runbum makamman ‘yan ta’addan.

Makamman sun hada da manyan bindigogi da harsashai, da ababe masu fashewa.
Tun a cikin shekara 2015 ne Burkina faso ke fama da matsalar tsaro da ake dangantawa da mayakan dake ikirari da sunan jihadi.

Alkalumman da MDD, ta fitar sun nuna cewa hare haren da ake kaiwa kasar sun yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, tare kuma da tilastawa kimanin 500,000 yin gundun hijira.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu