Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Gudanar Da Bikin Ranar Kare Hakkin Dan Adam Ta Duniya A Nigeria


Rahotanni da suka fito daga Nigeria sun bayyana cewa Nigeria ta bi sahun takwarorinta na Duniya wajen raya ranar 10 ga watan Disamba ta kare hakkin dan Adam na duniya, a daidai lokacin da hakkin furta albarkacin baki, hakkin da mulkin Demkuradiya ya bawa dan kasa ke fuskantar barazana a kasar.

Yanzu a Nigeria fadin albarkacin baki ba abu ne mai sauki ba, wadanda suke bude baki su fadi ra’ayoyinsu a da, yanzu dole su sanya linzami, domin kaucema abin da ka iya biyo baya, kuma wannan ya yazo ne bayan dokar hana furta kalaman batunci da majalisar dokokin kasar take aiki a kai da ta jawo ce-ce ku -ce a kasar.

Sai kuma wani kudurin da ya shafi yada karya ta hanyar Internet , da kuma kudurin da aka fitar na neman a rika sanya ido a sakwannin da ake aikewa a shafukan yanar gizo gizo.

Daga lokacin rantsar da gwamnatin Muhammadu Buhari zuwa yanzu ta ci gaba da nuna rashin jin dadi game da yadda wasu ke sukanta, inda wani dan adawa ke bayyana gwamnatin a matsayin ta soji amma da sunan ta demukuradiya.

Barazana da kame abokan hamayyar siyasa da yan jaridu da malamai da ma wasu yan kasa da ke sukar gwamnati ta kafafen sada zumunta da sauran hanyoyi na al’ada da aka saba yana kara karuwa sosai da kuma jefa fargaba cikin zukatan alumma.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu