Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Gudanar Da Gangamin Neman Sakin Shekh El-Zakzaky A Iran


A wannan asabar ce aka gudanar da gangamin neman a saki jagoran ‘yan uwa musulmi mabiya mazhabar shi’a a Najeriya Shekh Ibrahim Yakubu El-zakzaky a gaban Ma’aikatar harakokin wajen jamhoriyar musulinci ta Iran

Mahalarta gangamin sun nuna damuwarsu game da umarnin da kotun dake sauraran shari’arsa ta bayar na sauya masa wuri daga hanun jami’an tsaron farin kaya na DSS zuwa gidan kurkuku, inda suke ganin cewa hakan na iya illa ga lafiyarsa.

A watan Dicembar 2015 ne Sojojin Najeriya suka kai farmaki gidan shekh Ibrahim Yakubu Elzakzaky, inda suka rusa gidansa dake Gyallesu da kuma Husainiya Bakiyatullah da kuma kashe ‘ya’yansa guda uku gami da mabiyansa sama da dubu guda.

Bayan haka gwamnati ta kafa kwamiti domin sanin hakikanin abinda ya faru, yayin gabatar da shaida a gaban kwamitin lauyan gwamnatin Kaduna ya tabbatar da cewa an bizne gawawwakin mabiya sheikh Zakzaky 347 da sojoji suka kashe a lokacin, bayan kamala bincike da kuma gabatar da rahoto, gwamnatin kaduna karkashin gwamna Nasiru El-rufa’I ta ki aiki da shawarar da kwamitin ya gabatar, sannan baya ga hakan an gurfanar da Shekh El-zakzaky da mai dakinsa Malama Zinatu a gaban kotu, inda kotun ta bayar da umarnin sakinsa da kuma biyansa diya tare da gina masa gida amma gwamnatin El-rufa’I ta ki bin umarnin kotun.

Duk da rashin lafiyar da yake fama da ita sanadiyar harsashin da yake cikin jikinsa, kwatsam sai kotun dake saurarar shari’arsa a jihar kaduna ta bayar da umarnin sauya musu wuri daga hanun jami’an tsaron farin kaya na DSS zuwa gidan kurkurku, lamarin da ya kara sanya damuwa ga mafiyansa da ma wasu al’ummar kasar ta Najeriya.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu