Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

AN GUDANAR DA GASAR FARETIN YAN MAKARANTUN FUDIYYA A DAI'RAR KADUNA.....

A jiya Lahadi 15-12-2019 ne a ka gudanar da faretin yan makarantun fudiyya a da'irar kaduna.

Bayan an gudanar da zayen su dalibai makarantun fudiyya da misalin karfe 2:00pm na ranar yau Lahadi sai a ka gudanar da Salloli da cin abinci a kayi hutu na gajeren lokaci sai a ka fara gudanar da gasar faretin. 

An gudanar da gasar faretin ne tsakanin makarantu daban daban suka halarci gasar, ga je rin sunan sa nan kamar haka.

Madarassatul, Ahlul-Bayt Rigasa.
Muassatul Zainabul Kubra Hayin Rigasa.
Fudiyya Uguwan Rimi.
Fudiyya Central.
Ikamatul Deenil Islma.
Fudiyya  Uguwan Mu'azu.
Fudiyya Rigasa.
Fudiyya Rigachikun.
Madarassatul Fatimatul Zahra.
Fudiyya Badiko.
Fudiyya Barnawa.
Fudiyya Dan dami


An gabatar da gasar faretin ne a kan
Sharudda kaman haka. Iya taka rawan faretin. Sanan da iya sanya kaya dakuma kula da tsaftan kayan. Sanan da kuma wake ga annabi Muhammad (s.a.w.a). 
Hakika yaran suntaka rawan gani sanan kuma sun Isar da sako a inda suka nuna ba jin ta da burgewa ga Jama'a masu kallo.

Bayan kammala faretin su yan makarantun sai wakilin yan uwa na kaduna Malam Aliyu Umar (Tirmizi) ya gabatar da jawabi ga mahalarta taron, bayan fara da yiwa Allah godiya da kuma bayyana maka su din taron, sai Malam ya dan yi maga game da halin da muka tsinci kai da ga mahukunta, sannan ya kara da cewa duk da cewa wasu suna ganin abin da akeyi kamar bai da muhimmanci Lallai yana da muhimmanci, kuma wadanda a ke yi dan su sun san yana da muhimmanci, a suna jin yadda yara ke cewa ba mu yafe ba kuma zamu rama. 

Kana jin yaro na cewa Wallahi ba mu yafe ba! Kuma zamu rama, ka kasan a kwai rigima, suma azzalumai sun sani, wannan muna yi ne dan su San cewa a kwai magana, abun da suka yi ba ya wuce ba kenan, mu mun biku a wani lokaci amma wadannan yaran ba su sanku ba, mu mun iya wa'azi, amma wa dannan yaran ba su iya wa'azi ba, ran da suka taho gareku wa'azin biki za su yi, saboda haka in kai ka na gani wannan abun bai da tasiri, to su makiya sun san yana da tasiri.

Sannan daga cikin muhimmancin sa shi ne taya Al'ummar Annabi (s.a.w.a) murnar zagayowar ranar da a ka haifi Annabi (S), kuma du Masoyin Annabi (S) ya gani zai ji dadi. Sannan a nunawa yara ba kawai karatu bane ya zama aikin makarantun ba, a'a da Nishadan tar da su, san a nuna musu shi Musulunci yawa zamani obatakin (over talking), ba dan muna musulunci sai mu ko ma mu rungume hannu ba, mu zama kamar yan Taliban ko yan Kala Kato ba, mu dinka wa yara kayan Islamiyya da hula ya rufe kunne. Malam ya ciga ba da kawo abubuwa na waye wa da tafiya da zamani a musulunce.


Bayan kammala jawabin sa ke da wuya sai ka raba takardar shaida (certificate) ga makarantun da suka halarci shi wannan gasa, sai ka fara raba kyautuka ga zakarun wannan gasa, gasu nan kamar haka:

FANIN WAKE SUNE KAMAR HAKA

Ikamatul Islam 1
Madarasstul Ahlul-Bayt 2
Zainabul Kubra 3

SAI BANGARAN (DRESS) WATO IYA SANYA TUFAFI
Ikamatul Deen Islam 1
Fudiyyah Uguwan Mu'azu 2
Sai mai biye musu
Fudiyyah Badiko 3

BANGARE FARETI
WANDA SUKAYI NA DAYA
Fudiyyah Central 1
Fudiyyah Unguwar Mu'azu 2
Fudiyyah Rigasa 3

Wakilin yan'uwa na da'irar kaduna Malam Aliyu Tirmiz ne ya ba da kofin, sannan
Akayi addu'a aka Sallami Kowa.
Anyi antashi Lfy.

Kaduna press
Bashir Kaduna✍️

Post a Comment

0 Comments

Close Menu