Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Gudanar Da Zanga -zangar Adawa Da Amurka A Kasar Iraki


Dubban magoya bayan kungiyar sa kai ta Hashdu sha’abi a kasar Iraki ne suka gudanar da zanga zanga a birnin Bagadaza domin yin tir da tsoma baki cikin harkokin kasar da Amurka take yi da kuma sabon takunkumin da Amurkan ta sanyawa wasu jagorori a kungiyar ta Hashdu sha’abi
Masu zanga zangar sun sanya wani katako a gefe hanya da ke rataye da hotununn shugaban Amurka Donald Trumph da na Binyamin Natanyaho na HKI da kuma Bin Salam yarima mai jiran gado na kasar Saudiya.

Mohammad Al’ rube’I wani dan majsalisa a kasar Iraki a wata hira da aka yi da shi ya yi tir da matakin rashin adalcin da Amurka ta dauka akan wasu daga cikin jagororin na dakarun sa kai na Hashdu sha’abi da kuma shiga sharo ba shanu da kasar Amurka take yi a harkokin gidan kasar.

Kasar Amurka ta sanya takunkumi kan wasu daga cikin jagorarin kungiyar ne bayan da ta zarge su da hannu wajen murkushe masu zanga zanga da aka yi a kwanakin baya a kasar Iraki

Post a Comment

0 Comments

Close Menu