Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Kammala Taron Dandalin 'Yan Gudun Hijira Na Duniya

An kammala taron dandalin 'yan gudun hijira na duniya na farko da aka shirya a birnin Geneva, ranar Laraba, inda aka yi alkawuran taimakawa 'yan gudun hijirar da ma al'ummomin da suka ba su mafaka.

Wata sanarwa da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) ta bayyana cewa, an cimma alkawura sama da 770 a fannoni daban-daban yayin taron, wadanda suka hada da samar da aikin yi, da makarantu ga yaran 'yan gudun hijira, da sabbin manufofin gwamnati, da sake tsugunar da 'yan gudun hijira, da makamashi mai tsafta.

Sauran sun hada da ababen more rayuwa, da taimakawa al'ummomi da kasashen da suka baiwa 'yan gudun hijira mafaka yadda ya kamata.

UNHCR ta ce, bangaren sassa masu zaman kansu ne suka yi alkawari mafi yawa, da ba’a taba ganin irinsa ba, dangane de mutanen da ake tilasta musu barin muhallansu.

A jawabinsa, babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi, ya ce, yanayin 'yan gudun hijira, zai tsananta ne, idan har muka yi watsi da su, ko muka ki hada kai ko muka ki yin aiki tare, ko muka yi watsi da al'ummomin da suka ba su mafaka.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu