Wakilan kasashe 200 da ke halartar taron kare muhali na Majalisar Dinkin Duniya a birnin Madrid na kasar Espaniya na ci gaba da tattaunawa cikin rishin samun fahimtar juna.

Taron wanda yakamata aka kammala a jiya Juma'a an tsawaitashi har ya zuwa yau Asabar saboda rishin rishin fahimtar junan da aka samu tsakanin kasashen, wajen rage hayaki mai illa ga muhali da maki biyu kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma a Paris a shekara ta 2015 ta tanada.

Kasashen China da Indiya da Japan da Amirka da Saudiyya sune kasashe da suka fi fitar da tururin hayakin mai guba, kuma babu ko daya daga cikinsu da ya amince da dokokin da taron ya tattauna kansu cikin makoni biyu.