Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

AN SABUNTA AIKIN TSABTACE KABARIN MAHAIFIYAR SU SAYYID ZAKZAKY (H) A YAU LAHADI


Cikin Sanyin Safiyar Yau Lahadi 15/12/2019  ne, 'Yan uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) na Majalisin Jushi da ke cikin garin Zariya, suka yi aikin shara da tsaftace muhallin makwancin Mahaifiyar Jagoran Harka Islamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

Shidai aikin sun saba suna gudanar dashi ne a ko wacce ranar lahadi, na ko wanne mako, a yau din bayan sun share tare da goge tayis din wurin, sun kuma yi addu'oi na musamman da nufin Allah ya kara mats rahama.

Kabarin Mahaifiyar na Shaikh Zakzaky na cikin wani gida ne a unguwar na Jushi, a ranar 21/12/2015 Elrufa'i ya sa aka rushe gidan, bayan ta'addancin da sojoji suka yi a kan Jagoran, na kashe mutum fiye da 1000 daga almajirai, 'ya'ya da danginsa, da rusa gidansa da suka yi.

Kamar yadda kuga wasu daga cikin hotunan aikin gayyar da a ka gudanar a safiyar yau lahadi.
.
Daga Ali Ibrahim Yareema
15 December 2019

Post a Comment

0 Comments

Close Menu