A yau juma'a 27/12/2019 yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky na da'irar kaduna, sun fitowa domin jaddada kira ga gwamnatin  Buhari da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda da take cigaba da tsarewa tsawon shekaru hudu, kimanin kwanaki 1,476 ba tare da laifin komai ba.


Sheikh Zakzaky na tsare tun bayan harin ta'addancin sojojin Najeriya bisa jagorancin Yusuf Tukur Burtai, karkashin gwamnatin Buhari a ranar 12/12/2015, da kaisan mabiyan sa sama da dubu, ciki har da ‘ya‘yansa uku, da dan yayan sa mai suna shamsuddeen, da kona yayar sa da ranta a gaban sa, suka tsare daliban sa daruruwa, da yiwa wasu fiyade.

A shekarar 2016 babban Kotun dake Abuja ta wanke shi, tace: baiyi laifin komai ba, asake shi. Gwamnatin taki.

Bayan duk wannan ta'addancin da gwamnatin buhari tayi na take hakkin dan adam taka, da cin zarafin su, sun ta kokarin sai sun kashe shi ta hanyar ciyar da shi da shayar da guba. Ga Kuma ma tsanancin rashin lafiyar da yake fama da ita, da iyalin sa. A haka su dauko daga inda suke tsare da shi a Abuja suka dawo da shi kaduna karkashin Nasiru El rufa'i, su ka fa haramtaciyar kotu wai suna tuhumar sa da kisan kai, yayin da a ka ja lokacin a na gudanar da haramtaciyar shari'a da nufin gubar da suka ciyar da shi ya yi tasiri a jikin sa.


Bayan daukar dogo lokaci a gudanar da wannan shari'a, kotu ta ba da umarnin a fita da shi waje domin kulawa da lafiyarsa, yayin da gwamnatin ta yi kutsen a can kasar Indiya tare da kawayenta na kasar waje, don ganin sun cike burinsu na ganin bayan sa. Hakan bai yu ba sai suka yan ke shawara dawo da shi gida Najeriya. Suka cigaba da tsare shi ba bisa ka'ida ba.

Yanzu haka dai Sheikh Zakzaky (H) yana tsare a gidan kurkukun Kaduna, tare da iyalansa, ga rashin lafiya, ga Kuma Harsha shi a jikin su, amma wannan gwamnatin tana nuna halin ko in kula.


Muzaharar dai ta daga ne da misalin 3:00pm dai dai a dan kano road dake kan titin Ali akilu road da ke na cikin garin kaduna, yayin da a kayi tafiya mai tsawo, a ka mike hanya a bita shatale-talen lived thing's zuwa bakin Dogo daura da fatan teka, yayin da a ka ka she muzahara a nan.