Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Saki Masu Zanga-Zanga Sama Da Dubu Biyu A Iraki


Majalisar Kolin ta Shari'ar kasar Iraki ta sanar da sakin mutane sama da dubu biyu da 600 daga cikin wadanda aka kama a zanga-zangar baya-bayan na nuna adawa da matsalar rayuwa da al'ummar kasar take yi.

Cikin wani bayyani da ta fitar a jiya lahadi, Majalisar ta ce tawagar gudanar da bincike na zanga-zangar da aka gudanar a kasar ta saki mutane dubu biyu da 626 daga cikin mutanan da jami'an tsaron kasar suka kama a yankuna daban-daban na kasar bayan gudanar da bincike tare da tabbatar da rashin samun da laifi.

Rahoton ya ce har yanzu ana rike da mutane 181 wadanda ake ci gaba da yi musu tambayoyi musaman ma kan wasu tuhume-tuhume da ake yi musu.

Tun a ranar 1 ga watan Oktoban da ya gabata ce al'ummar kasar Iraki ta fara gudanar da zanga-zangar nuna adawa da barnata dukiyar kasa, rashin aikin yi, da kuma rashin yiwa talakawa aiki daga bangaren gwamnati a binrin Bagdaza da kudancin kasar, to saidai a ranar 25 ga watan na oktoba zanga-zangar ta kara fadada zuwa yankuna daban-daban na kasar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu