Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Samu Raguwar Kashe ‘Yan Jarida A 2019


Wani rahoto da kungiyar kare hakin ' yan jarida ta duniya wato Reporters without Borders ( RSF ) ta fitar, ya nuna cewa, yan jarida 49 ne aka kashe a cikin shekara nan ta 2019.

Rahoton na shekara shekara da kunmgiyar ta fitar ya nuna cewa wannan su ne alkalumma mafi kankanci da aka tab samu a cikin shekaru 16 na kisan da ake wa ‘yan jarida a duniya.

Alkalumman sun kasance na farko a tarihi, idan aka kwantanta da gomman shekaru da suka gabata inda ake kashe ‘yan jarida kusan 80 a cikin ko wacce shekara a kasashen dake fama da yake yake irinsu (Yemen, Syria da Afganistan).

Saidai rahoton na RSF, ya nuna damuwa da yadda har yanzu aikin ‘yan jaridan ke gamuwa da cikas a wasu kasashe da ake zaman lafiya, kamar Mexico inda a bara aka kashe ‘yan jarida 10, da kuma yawaitar kame kame na ‘yan jarida day a karu da kasha 12% idan aka kwatanta da bara, wadanda rabinsu sun kasance ne a kasashen Sin, Masar da kuma Saudiyya.

A game da ‘yan jaridan da ake garkuwa dasu kuwa, rahjoton ya ce ‘yan jarida 57 ne akayi garkuwa dasu ye zuwa karshen wannan shekara.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu