Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Tashi Kunne Doki Babu Ci Tsakanin Bacelona Da Real Madrid A Jiya


Wannan ne wasan Clasico na 90 da aka buga a Camp Nou, kuma har yanzu kungiyoyin na kankankan a wurin nasara, inda kowaccensu ta ci wasa 72 a dukkanin wasannin Clasico na La Liga.

Real Madrid ce ta kankane minti 45 na farko sakamakon kokarin da 'yan wasan tsakiyarta Tony Kroos da Valverde suka yi. Ya yin da ita kuma Barcelona ta mamaye falle na biyu na wasan kafin Gareth Bale ya zira mata kwallo a raga, sai dai na'urar VAR ta ce Mendy ya yi satar gida ne.

An bai wa Barcelona katin gargadi sau uku a minti 45 na farko, abin da ke nuna cewa ba ta ji dadin zagayen ba. Ita ma Madrid an ba ta guda biyar kuma duka a minti 45 na biyu.

Tun kafin wannan wasan kungiyoyi guda biyu ne a saman teburi da maki 35 kowaccensu, amma Barcalona tana saman Madrid da tazarar kwallaye guda biyu.

Sevilla ce ke biye masu a mataki na uku da maki 31, yayin da babbar abokiyar hamayyarsu Atletico Madrid ke mataki na biyar da maki 29.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu