Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Yanke Wa Jami’an Tsaro 27 Hukuncin Kisa A Sudan

Wata kotun Sudan, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu jami’an leken asirin kasar su 27, kan azabtarwa da kuma kisan wani dan zanga zanga a cikin watan Disamba na 2018.

Kotun dai ta tuhumi jami’an su 27 da hannu a azabtarwa ta hanyar duka da kuma kisan mutumin wanda malamin makaranta ne, mai suna Ahmed al-Kheir Awadh, a karshen watan Janairu na bara a yankin Kassala dake gabashin kasar.

A ranar 19 ga watan Disamba ne 2018, ne daruruwan ‘yan Sudan, suka fara zanga zanga a sassa daban daban na kasar, biyo bayan matakin gwamnati na kara farashin bredi a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tattalin arziki, lamarin da daga bisani ya rikide ruwa ga boren kin jinin gwmanatin Omar Al-bashir.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne sojojin kasar ta Sudan, suka kifar da mulkin Albshir wanda bayan shafe sama da shekara 30 yana mulkin kasar sakamakon matsin lamba na masu zanga zangar neman ya sauka daga mulki.

A wani rahoto data fitar, kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta ce kimanin masu bore 177 ne aka kashe a kasar ta Sudan.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu