A yau Talata ne wata kotu ta musamman a kasar Pakistan ta yanke hukuncin kisa ga tsohon shugaban kasar na soja Pervez Musharrafa, wanda a halin yanzu ya ke zaune a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Lauya mai tsayawa gwamnatin kasar ta Pakistan Salman Nadeem ya bayyana cewa; An sami Musharraf da laifin keta ayar dokar tsarin mulkin kasar Paksitan ta 6 na cin amanar kasa.

Tun a 2014 ne dai aka fara yi wa Musharraf shari’a akan dokar ta baci da ya kafa a ranar 3 ga watan 2007.

A wancan lokacin ne Musharraf ya kafa dokar t abaci domin tsige shugaban kotun koli ta kasar Iftikhar Muhammad Chaudry, lamarin da ya jawo fushi a tsakanin lauyoyi da ma’aikatan shari’a na kasar da kuma gagarumar Zanga-zanga.